Man City ta dage kan Enzo Fernandez, Sao Paulo da West Ham na neman Vardy

Manchester City za ta biya Chelsea sama da fam miliyan 120 don sayen ɗanwasan tsakiyan Argentina Enzo Fernandez idan ta iya ƙulla yarjejeniya kafin rufe kasuwar musayar ƴan wasa. (Telegraph – subscription required)
Chelsea ta sanya farashin kusan fam miliyan 100 kan ɗanwasan gefen Portugal Pedro Neto, mai shekara 26, wanda ake rade-radin cewa ƙungiyar Al-Hilal ta Saudiyya za ta ɗauke shi. (Mail)
Manchester City da Arsenal da kuma Tottenham suna zawarcin Neto, wanda ya koma Chelsea kan fam miliyan 54 daga Wolves a 2024. (Metro)
An bai wa Manchester United damar sayen dan wasan tsakiyan Sifaniya Marc Casado, mai shekara 22, wanda Barcelona ta sanya a kasuwa. (Sport – in Spanish)
Duk da rashin son sayar da shi da Manchester United ta nuna, Galatasaray ta yi wa ɗanwasan tsakiyar Portugal Bruno Fernandes tayin albashin fam miliyan 18.3 a kowace kakar wasa – ninki biyu na albashinsa na yanzu, a wani mataki na neman shawo kanshi ya bar Old Trafford. (Telegraph)

Post masu alaƙa

Mahaifin Lionel Messi, Jorge, ya rasu yana da shekara 68

Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya – Infantino

Kofin Duniya: Argentina ta tsallaka zuwa kwata-fainal bayan doke Masar