Home » INEC Ta Sake Tabbatar da Ranar Yin Zaɓuka a Wasu Jihohin Najeriya

INEC Ta Sake Tabbatar da Ranar Yin Zaɓuka a Wasu Jihohin Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta jaddada cewa, zabukan da za ta sake yi a jihohin Adamawa, Kebbi da sauran jihohi, za a gudanar da su a ranar 15 ga watan Afrilun wannan shekarar.

Majiyarmu ta ruwaito cewa, hukumar ta INEC ta ayyana zabukan gwamna na jihohin Kebbi da Adamawa a matsayin zabukan da ba a kammala ba, inda hukumar ta ce, za a sake gudanar da zabe a wasu mazabu a jihohin.

Babban jami’in yada labarai na hukumar INEC, Mista Rotimi Oyekanmi ya sanar da hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, inda ya ce, za a gudanar da zabukan kamar yadda hukumar ta tsara.

Oyekanmi ya ce, tun daga wancan lokacin, babu wani abu da ya sauya.

Hukumar ta INEC ta yanke shawara cewa, duk zabukan gwamna da na ‘yan majalisar dokoki da za a sake yi, za a gudanar da su ne a ranar 15 ga watan Afrilu. 

INEC ta dai ayyana zabukan gwamna na jihohin Kebbi da Adamawa da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na 2023, a matsayin zabukan da ba a kammala su ba, inda ta ce, za a sake gudanar da zabukan a wasu mazabun da ke jihohin.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?