Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin FA na shekarar 2026 bayan doke Chelsea 1-0.

Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao a baya-bayan na, inda take harin kofin Firimiya da Arsenal ke kan teburi.

Zuwa yanzu Pep Guardiola ya lashe kofuna 20 cikin shekaru 10 a Manchester City.

Post masu alaƙa

Yan sandan Kano sun gaiyaci Aminu Warkal kan zargin nuna bindiga.

2027: Sama da mutum 10,000 sun nuna goyon bayansu ga Tinubu da Namadi a mazabar Limawa

Gwamnonin Arewa maso Gabas na yin taro a Maiduguri