Daga: Rabi’u Hashim Rabi’u
Ƙasar Isra’ila na ci gaba da shan suka mai zafi daga bangarori daban-daban na duniya bayan sanar da katse duk nau’in tallafi daga shiga zirin Gaza.
Matakin na Isra’ila ya zo ne a daidai lokacin da ake matukar bukatar kayan abinci saboda azumin watan Ramadan.
Kasashen da suka shiga tsakani wajen ganin an tsagaita wuta Qatar da kuma Masar sun zargi Isra’ilar da saba yarjejeniyar ta tsagaita wuta da aka sanya wa hannu tare da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki.
EU ta bukaci dakatar da farmakin Isra’ila a yamma da kogin Jordan
- An Kama Ɗan Ƙasar Angola Kan Safarar Miyagun Kwayoyi A Najeriya
- EFCC Ta Tabbatar Da Yin Kame A Wani Otal A Neja
Kashin farko na yarjejeniyar ya bada damar an rika shigar da kayan agaji zirin bayan shafe watanni ana fama da bukatarsu musamman ma magunguna da abinci ba tare da samu ba.
Kungiyar Hamas ta zargi Isra’ila da kokarin kauce wa kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar bayan ya kare a ranar Asabar.
Isra’ila ta bukaci tsawaita yarjejeniya har bayan Ramadan
Isra’ila ta yi ikirarin cewa wani sabon kudurin Amurka ya bukaci a tsawaita kashin farko na yarjejeniyar sakamakon Ramadan maimakon shiga kashi na biyu wanda da zarar an fara shi babu koma wa yaki.