Home » Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza

Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza

Rundunar sojin Isra'ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.

Jiragen yakin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a arewaci da kudancin zirin Gaza duk da kiran da dakarunta suka yi kan cewa za ta bayyana yankunan tudun mun tsira ga fararaen hula da ake ci gaba da ritsawa da s. Ma’aikatar lafiya ta Falalsdinawan ta ce an halaka mutane da dama a sassa daban daban na zirin.

An ga motocin yakin Isra’ilan na shiga yankin Netzerim da nufin yi wa zirin kofar rago a daidai lokacin da ministan tsaron Isra’ilan Israel Kanzt ke gargadin karshe ga mazauna zirin cewa su fice daga cikinsa idan ba haka ba komai ya samesu kar su zargi kowa sai kawunansu.

“Kowane taki a zirin Gaza filin daga ne. Dakarun sojinmu za su shiga shi don neman ‘ya’yanmu da ake garkuwa da su. Ba za su sake yarda a dinga yin garkuwa da fararen hula ana kai musu hare haren sunkuru ba. Domin za mu ci gaba da kai hare haren kan mai uwa da wabi babu kakkautawa.”

Tuni dai kungiyar Hamas ta lashi takobin fafatawa da dakarun na Isra’ila duk da aniyarsu ta ci gaba da mutunta tsagaita wuta idan Isra’ila ta dakatar da abin da suka kira kisan kare dangi na ba gaira ba dalilin da ta ke yi wa Falasdinawa kamar yadda kakakin baradenta Abu Ubaida ke fadi.

Siyasa
Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza
Mahmud Yaya Azare
Sa’o’i 13 da suka wuceSa’o’i 13 da suka wuce
Rundunar sojin Isra’ila ta fara samame ta kasa a kudancin zirin Gaza lamarin da ya jawo martini daga kasashen duniya.

Jiragen yakin Isra’ila sun ci gaba da luguden wuta a arewaci da kudancin zirin Gaza duk da kiran da dakarunta suka yi kan cewa za ta bayyana yankunan tudun mun tsira ga fararaen hula da ake ci gaba da ritsawa da s. Ma’aikatar lafiya ta Falalsdinawan ta ce an halaka mutane da dama a sassa daban daban na zirin.

An ga motocin yakin Isra’ilan na shiga yankin Netzerim da nufin yi wa zirin kofar rago a daidai lokacin da ministan tsaron Isra’ilan Israel Kanzt ke gargadin karshe ga mazauna zirin cewa su fice daga cikinsa idan ba haka ba komai ya samesu kar su zargi kowa sai kawunansu

‘Yan Gaza na sake yin kaura saboda hare haren Isra’ila’Yan Gaza na sake yin kaura saboda hare haren Isra’ila
Hoto: Mahmoud Issa/REUTERS
“Kowane taki a zirin Gaza filin daga ne. Dakarun sojinmu za su shiga shi don neman ‘ya’yanmu da ake garkuwa da su. Ba za su sake yarda a dinga yin garkuwa da fararen hula ana kai musu hare haren sunkuru ba. Domin za mu ci gaba da kai hare haren kan mai uwa da wabi babu kakkautawa.”

Tuni dai kungiyar Hamas ta lashi takobin fafatawa da dakarun na Isra’ila duk da aniyarsu ta ci gaba da mutunta tsagaita wuta idan Isra’ila ta dakatar da abin da suka kira kisan kare dangi na ba gaira ba dalilin da ta ke yi wa Falasdinawa kamar yadda kakakin baradenta Abu Ubaida ke fadi.

Hare haren Isra’ila sun tagaiyara Falasdinawa a GazaHare haren Isra’ila sun tagaiyara Falasdinawa a Gaza
Hoto: Hatem Khaled/REUTER
Masu gwagwarmayar Falalsdina sun yi matukar mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da Isra’ila wacce ta kai ga sakin fursunonin yaki daga bangarorin biyu. A yanzu duniya ta ga ko waye ke son ci gaba da zub da jini a cikinmu. Don haka muke kira ga kasashen duniya da su tashi haikan don taka wa Isra’ila da Amurka birki kamar yadda muke kara tabbatar da shirin mayakanmu na tunkararsu da ci gaba da fafatawa da su har sai mun tsarkake garuruwanmu daga kazantar wadannan ‘yan mamayar
Tuni dai kungiyar Hamas ta yi ruwan rokoki kan garuruwan Isra’ila. A yayin da ita ma kungiyar Al Houthi ta Yemen, ta harba tarin rokoki kan birnin Tel Aviv da Jerusalam, lamarin da ya razana mazaunanasu suka yi ta tserewa zuwa ramukan karkashin kasar da aka tanada don gudun bacin rana.

Hatta shi kansa firaim ministan Benjamin Natenyahu, sai da aka garzaya da shi cikin maboyarsa yadda daga can din yake barzanar cewa mayakan na Houti za su gani a kwaryarsu.

Harin ‘yan tawayen Houthin na Yemen na zuwa ne bayan gargaɗin da Donald Trump na Amurka ya yi cewa duk wani hari da suka kai walau kan manufofin Washington a gabas ta Tsakiya ko kuma kan Isra’ila kai tsaye Iran ce za ta ɗanɗana kuɗarta.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?