Rundunar yan sandan jihar Kano, ta kama wasu mutane 5 da ake zarginsu da hada kai wajen yin garkuwa da wani matashi mai suna , Muhammad Bello dan shekaru 21, mazaunin garin Zakirai dake karamar hukumar Gabasawa Kano, inda masu garkuwa da mutanen suka nemi kudin fansar naira miliyan 15 kafin su sake shi.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ga manema labarai ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sanarwar ta ce tun bayan samun korafin ne kwamishinan yan sandan jihar Kano, ya tashi dakarun yan sanda karkashin jagorancin shugaban sashin dake yaki da masu garkuwa da mutane CSP Bala Shu’aibu, da su tabbatar da sun kubutar da matashin tare da kama wadanda suka aikata laifin.
Sanarwar ta kara da cewa jami’an yan sandan sun yi amfani da sabbin dabarun aiki wanda kwamishinan yan sanda ya tsara har aka samu nasarar kubutar dashi tare da kama mutane 5.
- Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a zirin Gaza
- Zargin Nadin Mukamai Ba Bisa Ka’ida Ba Ya Kunno Kai A Hukumar Alhazan Najeriya NAHCON
Cikin wadanda rundunar ta kama sun hada da Tukur Lawan wanda akafi sani da Maikudi , Ado Usman da akafi sani da Ruwa , Sunusi Sirajo, Ummulkhairi Ibrahim da kuma Habiba Shu’aibu.
Binciken da yan sandan suka gudanar kan wadanda ake zargin an samu Bindiga guda 1 a wajensu da kuma kudin fansar da suka haka rami suka binne har naira miliyan hudu da dubu dari takwas da hamsin (N4,850,000:00) .
SP Kiyawa ya kara da cewa yanzu haka dai an dawo da su babban sashin gudanar da binciken manyan laifukan dake shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai don fadada bincike akansu kuma da Zarar an kammala gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu bakori, ya godewa jami’an yan sandan da suka yi wannan aikin tare da neman hadin kan al’umma a koda yaushe.
