Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Ofishin NLC

Rahotanni daga hedikwatar Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC na cewa gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai sun yi wa hedikwatarta da ke Abuja, kawanya.

NLC ta ce jami’an tsaro sun isa ginin hedikwatar ta su ne da ake kira Labour House.

Shugaban sashen hulda da jama’a na NLC Benson Upah ya ce jami’an sun karya kofar ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suka kwashe  littattafai da takardu.

Benson Upah ya ce, jami’an sun ce suna neman wasu takardu da aka yi amfani da su yayin zanga-zanga a Najeriya.

NLC ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, sai dai ta yi kira da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar ta su.

Post masu alaƙa

Rundunar yan sandan shiyya ta daya ta kama Mutane biyar kan zargin jabun magunguna da sojan Gona.

Kwalejin sojan ruwa dake Dawakin-Tofa ta kara karfafa hadin gwiwar aiki tare da rundunar yan sandan Kano.

Kwastam ta kama harsasai 3,300 da kayayyakin fasa-ƙwauri a Seme