• Home  
  • Jamiyyar APC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance
- Babban Labari - Siyasa

Jamiyyar APC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu rijistar zama ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidan gwamnati da ke Fatakwal. Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a ranar Juma’a da […]

Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu rijistar zama ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidan gwamnati da ke Fatakwal.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a ranar Juma’a da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Fubara ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne da nufin bun\ƙasa haɗin kai da ci gaban jihar Ribas.

Fubara ya ce samun daidaito da jam’iyya mai mulki a matakin tarayya ya zama wajibi don tabbatar da zaman lafiyar siyasa da kuma hanzarta ci gaba a faɗin jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa a yanzu da jihar Ribas ta haɗe a ƙarƙashin inuwa ɗaya da gwamnatin tarayya, aikin da ke gabansa na ƙarfafa jam’iyyar APC da tabbatar da tafiyar siyasa cikin lumana a 2027 ya ƙara fitowa fili kuma a yanzu ana ganin haƙar za ta iya cimma ruwa.

Bikin ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo (SAN).

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai