Jihar Jigawa za ta gudanar da bukukuwan cika shekaru 35 da kafuwarta, inda gwamnatin jihar ta shirya karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar.
An ƙirƙiro Jihar Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan 1991, a lokacin mulkin tsohon shugaban mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Gwamnatin jihar ta amince da gudanar da addu’o’i na musamman a Masallatan Juma’a da ke faɗin jihar domin tunawa da ranar kafuwar jihar.
Za a yi addu’o’in ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyar limaman Masallatan Juma’a, majalisun masarautu da Majalisar Malamai ta jihar.
Haka kuma, gwamnati ta amince da shawarwarin wani kwamiti da Mataimakin Gwamna, Injiniya Aminu Usman, ya jagoranta.
Daga cikin shawarwarin akwai samar da tsari na musamman da zai riƙa jagorantar bukukuwan tunawa da ranar kafuwar jihar a duk shekara.
Haka kuma, za a samar da tsarin bayar da lambobin yabo ga mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen ci gaban jihar.
Gwamnati ta ce za a karrama waɗanda suka kafa jihar, tsoffin shugabanni, ma’aikatan gwamnati, sarakunan gargajiya da sauran mutane da ƙungiyoyi.
Bikin zai kuma bai wa al’ummar jihar damar duba irin ci gaban da Jigawa ta samu cikin shekaru 35 da kuma zaburar da jama’a su ƙara haɗa kai wajen gina jihar.