Cutar jijjiga lalura ce da mata ke fuskanta a lokacin haihuwa, inda suke jijjiga da yunƙurin tauna harshe da sauran su.
A wani rahoto da ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta fitar a watan Oktoban shekarar 2024 game da hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar jijjiga.
Hukumar kula da bada shawarwari akan cutar jijjiga ta kasa” ta ce mutuwa lokacin haihuwa na cikin manyan matsalolin da ɓangaren kiwon lafiya ke fuskanta a ƙasar nan.
Rahoton ya ƙara da cewa cutar na cikin abubuwa biyar da suke jawo mutuwar mata wajen haihuwa,
Rahoton ya ce cutar ce ke sanadiyar kashi 17 cikin 100 na mutuwar mata wajen haihuwa, inda rahoton ya ce za a iya kiyaye aukuwar mutuwar ta hanyar amfani da ƙa’idojin da suka dace.
Cutar ta jijjiga tana da alamun da mai haihuwa za ta fara nunawa, wanda ake kira pre-eclampsia, kamar hauhawar bugawar jini, kafin mace ta fara jijjigar.
A duniya, aƙalla mata 700,000 ne suka rasuwa a sakamakon jijjiga a shekara, kuma sama da abin da ke cikin ko kuma jarirai 500,000 suke mutuwa, wanda yake daidai da rasa aƙalla rasuwa 1600 a kullum, kamar yadda rahoton ma’aikatar lafiya ya nuna.
Domin jin abin da ke jawo jijjigar, Muhasatvr ta tuntuɓi Dokta Maryam Muhammad, wadda likitar mata ce a Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi wase {Asibitin Nassarawa} ta ce cuta ce da mafi yawancin bincike ya nuna ba a san me yake kawo ta ba, “amma akwai abubuwan da suke da dangantaka da ita kamar hawan jini da masu ciki, sanna akwai mabiyiya, wato abin da ake kira uwa da take fitowa bayan an haifi yaro. Ana tunanin matsalar da ke jawo cutar tana tattare da ita mabiyiyar.”
Sai dai duk da yadda cutar ke cin mata, har yanzu ba a gano takaimaimen abin da ke jawo ta ba. “Kamar cutar maleriya an san cizon sauro ke jawo ta, amma ita wannan cutar akwai dai abubuwan da ake lura da su, idan kana da su, akwai yiwuwar za ka tsinci kanka a wannan cutar, amma takaimame abin da ke jawo ta, ba a sani ba,” in ji Dokta Maryam.
Dokta Maryam ta lissafa wasu abubuwa da ta ce masu su suna cikin hatsarin kamuwa da cutar a lokacin haihuwa:
Mata masu ƙananan shekaru da suka samu cikin farko da waɗanda shekarunsu suka ja, suna cikin waɗanda suke cikin haɗarin kamuwa. Ƙasa da shekara 18 da sama da shekara 35.
Masu hawan jini. Hawan jini na cikin manyan abubuwan da ke alamta samuwar jijjiga.
* Masu ɗauke da cutar sukari.
* Da ɗauke da cikin ƴan biyu ko ƴan uku ko sama da haka.
* Wadda mahaifiyarta ko ƴan uwanta ko ta taɓa yin cutar a baya.
* Cututtukan da garkuwar jikin mutum ke faɗa da garkuwar jikinsa.
A game da hanyoyin da ya kamata a bi domin kare faɗawa cikin wannan yanayi na tsinkau-tsinkau, Dokta Maryam ta ce zuwa asibiti da sauri na da matuƙar muhimmanci.
A cewarta, “Abu na farko shi ne cutar tana bayar da alama. Hawan jini na ckin manyan alamu. Don haka da mace ta samu ciki yana da kyau ta fara zuwa awo. Zuwa awon ne zai sa a riƙa auna yanayin jinin, da an ga jinin ya fara hawa sai a san me za a yi domin a daƙile cutar cikin sauri.”
Marasa lafiya da ke fama da wannan ciwo sukan nuna alamomi kamar haka, rashin yin fitsari a kan lokaci da ɗaukewar numfashi da kumburin ƙasa da dunduniya da motsewar tsokar jiki da tashin zuciya ko amai. Da zarar ka ga wannan alamu, akwai buƙatar wankin ƙoda ko yin dashen wata ƙodar domin cigaba da rayuwa.