Home » Fada Ya Kaure A Sheka Bayan Mutuwar  Dan Daba

Fada Ya Kaure A Sheka Bayan Mutuwar  Dan Daba

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Mujahid Wada Musa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta kama matasa masu tarin yawa, a unguwar sheka, sakamakon ricikin fadan daba da ya kaure a tsakanin su.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ricikin ya barke ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu Sheka Babban Layi, da ake zargi da laifin fashi da kuma laifukan daba a unguwar Sheka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin yana cikin gungun matasan da ake kira da Yan shida wadanda suka addabi Sheka da fashi da kuma fadan Daba.

Al’ummar unguwar ne suka kama shi sannan suka karya kafarsa daya tare da yiwa dayar raga-raga lamarin ya da kai ga ya rasa ransa kamar yadda kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano ya sanar.

Rundunar ta kara da cewa abokan marigayin ne suka fito daukar fansar , Inda fadan Daba ya rincabe har aka kama mutane ma su yawa.

Wakilin mu da ya ziyarci unguwar ya bayyana mana cewar al’amura sun lafa sakamakon baza jami’an tsaro da aka yi a yankin don tabbatar da zaman lafiya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?