Home » Masana Su Fara Hasashen Lokacin Tashin Duniya

Masana Su Fara Hasashen Lokacin Tashin Duniya

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Agogon da ke hasashen tashin duniya ya ƙara matsawa da daƙiƙa ɗaya, inda yanzu ya rage daƙiƙa 89 ko kuma minti ɗaya da sakan 20 kafin tashin duniya, lokaci mafi kusa da ya taɓa kaiwa.

Ƙungiyar masu nazari kan harkokin kimiyya ta Bulletin of Atomic Scientist (BAS), wadda ke saita agogon a duk shekara, ta ce Agogon ya fara aiki ne tun a shekarar 1947, inda ya fara daga mintuna bakwai kafin tashin duniya, wanda kuma a bara, ba’a sauya shi ba daga daƙiƙa 90 da yake.

A cikin sanarwar da ƙungiyar mai zaman kanta da ke Chicago ta fitar, ta hannun shugaban kwamitin kimiyya da tsaro Daniel Holz, ta ce matsar da agogon da suka yi da daƙiƙa ɗaya, tamkar aikewa da saƙo mai ƙarfi ne a wani matakin gargaɗi ga dukkan shugabannin duniya.

A cewar Danial, ”Saboda duniya ta na ta ƙara kusantar faɗawa halaka, matsawa ko na daƙiƙa al’amari ne da ya kamata a ɗauka a matsayin alama da ke nuna tsananin haɗari, kuma gargadin cewa duk daƙiƙa ɗaya da ya wuce ya na ƙara mana kusanci ga faɗawa bala’i a faɗin duniya.”

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa ci-gaba da yaƙi a Ukraine wanda yanzu a ke kusantar shekaru uku bayan mamayar Rasha, zai iya rikiɗewa ya koma yaƙin nukiliya a kowanne lokaci saboda wani matakin gaggawa ko kuskure ko kuma rashin lissafi.

”Rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya na barazanar tsananta ya zama babban yaƙi ba tare da gargaɗi ko alamu ba,” in ji sanarwar.

Tawagar masu bincike kan kimiyyar sun kuma ce ”shirin dogon lokaci da duniya ta yi na magance sauyin yanayi ba ya tasiri sosai, ganin cewa akasarin gwamnatoci sun gaza aiwatar da tsarin samar da kuɗaden da ake buƙata domin daƙile ɗumamar yanayi.”

A fannin ilimin halittu, ƙungiyar BAS ta ci-gaba da cewa, ”cututtukan da ke ɓullowa da waɗanda ke sake dawowa na cigaba da yin barazana ga tattalin arziki, da al’umma da kuma tsaro a faɗin duniya”.

Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa ” jerin wasu sabbin fasahohi sun bunƙasa a bara, a wani yanayi da suka sa duniyar ta ƙara haɗari”.

”An yi amfani da tsarin da ake sanya ƙirƙirarriyyar basira cikin samamen da ake yi a Ukraine da gabas ta tsakiya, kuma wasu ƙasashe da dama sun fara yunƙurin sanya ƙirƙirarriyar basirar cikin ayyukan sojojinsu.”

Ƙungiyar ta jaddada cewa dukkanin waɗannan barazanar ”na ƙara tsananta ne saboda wasu dalilai kamar yaɗa labaran ƙarya, da labaran da ba su da tushe da ke kawo cikas ga tsarin sadarwa ya kuma toshe layin da ke tsakanin gaskiya da ƙarya.

A karshe BAS ta ce Amurka da China da Rasha na da ƙarfin haɗin gwuiwar da za su ruguza ɗan’adam baki ɗaya, adan haka ƙasashen uku na da alhakin fitar da duniya daga barazanar halaka.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?