Jam’iyyar PDP ta dakatar da tsohon gwamnan Jihar Ekiti Ayodele Fayose da tsohon gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, da wasu ‘ya’yanta biyu bisa zarginsu da yi wa mata zagon kasa.
PDP ta kuma tura gwaman Jihar Binuwe, Samuel Ortom zuwa ga kwamitin ladabtarwa bisa zarginsa da yi wa mata zagon kasa.
Sakataren PDP na kasa, Debo Ologunagba ne, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar.
Ologunagba, ya ci gaba da cewa, bayan da kwamitin zartarwar PDP na kasa bayan dogon tattaunawa kan abin da ya shafi jam’iyyar, bisa kundin tsarin mulkin PDP bna shekarar 2017 da aka sabunta ya tura Ortom zuwa ga kwamitin saboda zargin aikata zagon kasa.
Sauran wadanda ake zargin su ne Farfesa Dennis Ityavyar da Dakta Aslam Aliyu.