Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro

Ƙungiyar Kanawa Mazauna Birnin Tarayya Abuja ta gudanar da wani babban taro a ranar Lahadi, wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyar daga ƙananan hukumomin birnin.

Shugaban Kanawa Mazauna Abuja Initiative Group, Alhaji Ali Baba, ya ce wannan ne karon farko da ƙungiyar ta gudanar da irin wannan babban taro tare da haɗin kan mambobinta.

Ya ce manufar ƙungiyar ita ce ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobinta, taimaka wa al’umma da kuma inganta zumunci da fahimtar juna.

kungiyar dai tana burin taimakawa al’umma da samarwa da daliban suka kammala karatu guraben aiki a ma’aikatun gwamnati da kuma kamafanoni masu zaman kansu harma da tallafa musu da jari don dogaro da kansu.

Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana gamsuwarsu da yadda taron ya gudana, tare da yin alkawarin ci gaba da bai wa ƙungiyar goyon baya domin ganin ta cimma manufofinta.

Taron ya gudana cikin yanayi na annashuwa, inda mahalarta suka samu damar tattaunawa da juna tare da ƙarfafa zumuncin da ke tsakaninsu.

 

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.