Rimingado ya kaddamar da kwamitoci 9 da kan yaki da miyagun kwayoyi a Kano.

Shugaban kwamitin haɗin gwiwar hukumomi ta yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun kwayoyi a Kano, Muhuyi Rimingado, ya ƙaddamar da kwamitoci tara domin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da matsalar miyagun ƙwayoyi a jihar.

Rimingado ya buƙaci mambobin kwamitocin da su kasance masu jajircewa, tare da aiki kafada da kafada wajen ganin an cimma manufofin rundunar.

Ya ce nasarar yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi na buƙatar haɗin gwiwa, kyakkyawan tsari da ɗaukar nauyin kowa.

Ya bayyana cewa an kafa kwamitocin ne domin samar da ingantaccen tsarin tunkarar matsalar miyagun ƙwayoyi da kuma haɗa kan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.

An ƙaddamar da kwamitocin ne a ranar Juma’a, 21 ga Agusta, 2026.

Post masu alaƙa

Tinubu ya taya ‘yar Gombe murnar lasha gasar musabaka ta duniya

Mutanen da suka mutu a haɗarin kwale-kwale a Sokoto sun kai 48

Gwamnatin Jigawa ta fara gina sabuwar fadar Sarkin Dutse kan N2.6bn