Hukumar Bunƙasa Zuba hannun Jari ta Ƙasa, NIPC, ta ce suna haɗa kai da masu saka hannun jari daga ƙasar Jamus domin bunƙasa kasuwanci a tsakanin ƙasashen biyun.
Babbar Sakatariyar hukumar, Aisha Rimi, ce ta bayyana hakan a Abuja a yayin wata tattaunawa da wasu kamfanoni 22 daga ƙasar Jamus da Yammancin Turai waɗanda suka nuna sha’awarsu ta zuba hannun jari a ƙasar nan.
Kuma ana sa ran za su zuba kuɗin da zai kai yuro miliyan dubu uku.
Sakatariyar ta ce sun tattauna da masu ruwa da tsaki a jihohin ƙasar nan domin tattara bayanai game da ɓangarorin da za su samar da riba tare da miƙa bayanan ga masu son zuba hannun jarin.
Shi ma shugaban masu son zuba hannun a Najeriya daga ƙasar Jamus, Michael Schmidt, ya ce sama da kamfanoni 22 ne suka ziyarci jihohi daban-daban na ƙasar nan waɗanda kuma tuni suka nuna sha’awarsu ta zuba hannun jari a ɓangarori daban-daban na kasuwanci a ƙasar nan.