A ranar 14 ga watan Janairun shekara mai zuwa ta 2024 katafaren kantin nan na Shoprite zai rufe reshensa da ke jihar Kano. Yana ɗaya daga cikin manyan kantuna a Najeriya duba da shahararren wurin sayar da kaya na Ado Bayero Mall a nan birnin Kano.
An sanar da rufe babban kantin ne a cikin wata wasika ga ma’aikatansa, mai kwanan watan 7 ga Disamban shekarar da muke ciki ta 2023.
Shoprite, wanda ke karkashin Retail Supermarkets Nigeria Limited, ya bayyana a cikin wasikar cewa sun dauki matakin ne “bayan tantance yanayin kuɗi na kantin da kuma yanayin kasuwanci a yanzu”.
Kamfanin ya yi alƙawarin taimaka wa ma’aikatansa wajen nema musu sabbin damammaki a sauran wurarensu a fadin Najeriya.
Sannan kamfanin ya ce zai buɗe sabbin kantuna a cikin wata mai zuwa kuma za su yi maraba da duk wani tsohon ma’aikacinsu mai bukatar aiki da su.