Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce, ta cafke wata mata mai shekara 35 da ake zargi da soka wa wata ƙaramar yarinya wuƙa a cikinta, a yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Juma’a.
Sanarwar ta ruwaito cewa, matar mai suna Fatima ta ɗauki yarinyar ne zuwa wani gida da ba a kammala gininsa ba, inda a nan ne ta soka mata wuƙar daga bisani ta gudu ta bar ta.
Haka kuma ta cikin sanarwar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ƙara da cewa, bayan kama mijin matar ya yi iƙirarin cewa tana da matsalar ƙwaƙwalwa, kuma bai san wajen da take ba.
Ya kuma ce, sai dai daga bisani rundunar ta cafke ta ranar Alhamis a wurin da ta ɓoye a ƙauyen Dungulmi a ƙaramar hukumar Dutse ta jihar Jigawa.
Ya ce, har zuwa lokacin fitar da sanarwar su na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin wanda ya faru a ranar Lahadi, kuma wadda ake zargin ta amsa cewa ta aikata laifin.