Home » Kano: An gudanar da taron wayar da kai kan safarar bil’adama

Kano: An gudanar da taron wayar da kai kan safarar bil’adama

by Anas Dansalma
0 comment
kano

Ƙungiyar da ke yaƙi da safara da bautar da ƙananin yara NACTAL tare da haɗin guiwa da hukumar yaƙi da safarar bil’adama ta ƙasa NAPTIP, da sauran kwamitocin karta kwana da ke yaƙi da wannan ɗabi’a, sun gudanar da taron wuni ɗaya domin wayar da kan al’umma kan matsalolin safar bil’adama da shigi da fici ba bisa ƙa’ida ba a nan jihar Kano.

Taron ya gudana ne a cibiyar koyar da mata sana’o’i da ke kan titin Court Road a unguwar Gyaɗi-Gyaɗi a nan birnin Kano.

Wakilinmu Ismail Sulaiman Sani ya halarci wurin taron ga kuma rahoton da ya haɗa mana a kai.

Shugaban Ƙungiyar ta NACTAL Muhammad Mashi, ya ce, makasudin taron shi ne haɗakai da hukumomin gwamnati da jami’an tsaro wajan daƙile wannan mummunar ɗabi’a da ta riga ta zama ruwan-dare a ƙasar nan.

Mashi ya ce, yana kira ga al’umma da su ba wa hukumomi da ƙungiyoyi irin nasu haɗin kai domin kaiwa ga nasara.

Babbar sakatariya a ma’aikatar mata, da ƙananan yara da kuma masu buƙata ta musamman ta jihar Kano, Sa’adatu Sa’idu Bala, ta bayyana muhimmancin irin wannan wayar da kai, duba da yanayin matsin tattalin arziki da ake fama da shi a yanzu.

An dai rufe taron da ƙaddamar da kwamitin wakilai daga ɓangarorin al’umma waɗanda za su bayar da gudummuwa wajen tabbatar da manufar da aka a gaba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi