Shugaban gamayyar kasuwannin Sabon Gari ta Abubakar Rimi da Singa da Kasuwar Galadima da kuma ƙungiyar Kawo Ƙarshen Fatara a jihar Kano, wato Kano Alternative for Poverty Eradication sun yaba wa kwamishinan ‘yan sandan jihar nan, CP Mohammed Usaini Gumel saboda gudunmowar da yake bayarwa wajen ci gaban matasa da wanzar da zaman lafiya a jihar Kano.
A jawabinsa, shugaban gamayyar kasuwannin Mallam Abdul Bashir Hussaini, ya ce sun kai wa kwamishinan ‘yan sandan ziyara ne domin nuna jin daɗinsu da ƙoƙarin da yake yi wanda hakan ne ya sa aka samu zaman lafiya da tsaro a kasuwannin.
Sannan ya tabbatar da aniyarsu, a matsayinsu na ‘yan kasuwa, wajen ci gaba da bai wa kwamishinan haɗin kai a ƙoƙarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya a jihar nan.
A yayin da shi kuma kwamishinan ‘yan sandan yake nasa jawabin ga jagoran ‘yan kasuwar da tawagarsa, ya ce tun bayan kama aiki da ya yi a matsayin kwamishinan ‘yan sanda ya mai da hankali ne wajen buɗe ƙofa ga gudunmuwa daga al’umma da nuna ƙarewa a aikinsu da suke, sai kuma rashin aminta da kowanne irin nau’i na cin hanci da rashawa a yayin aiki.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa, zai tabbatar da cewa zaman lafiya ya wanzu a kowanne gida ake da shi a faɗin jihar nan tare da sanar da al’umma cewa ƙofarsa a buɗe take domin karɓar shawarwari daga al’umma.