Rukuni na hudu, ɗauke da ɗalibai 150 da gwamnatin Kano mai ci ta ɗauki nauyin karatunsu a ƙasashen waje sun tashi zuwa ƙasar India domin yin karatun digiri na biyu a fanni daban-daban.
Tallafin karatun na daya daga cikin manya-manyan alkawura da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi lokacin yakin neman zaben sa.
Tuni dai aka fara shirin inda a yau Juma’a rukuni na huɗu ya tashi zuwa kasar India daga filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.
Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan tashin ɗaliban, Kwamishinan Ilimi mai Zurfi na jihar, Dr Yusuf Kofarmata, ya ce za su sauka a Legas ne kafin su wuce zuwa India.
A cewar sa, da saukar su a India, za a kwashe su zuwa jami’o’i daban-daban da za su yi karatun su a fannonin ilimi daban-daban.