Kano: Kotu ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC ta shigar kan nasarar Sanata Rufa’i Sani

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar nan ta kori ƙarar da jam’iyyar APC ta shigar don ƙalubalantar Sanata Rufa’i Sani Hanga a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanatan Kano ta tsakiya.

Abdussalam Abdulkarim da aka fi sani da AA Zaura na jam’iyyar APC ne, ya shigar da ƙarar saboda dalilai da dama ciki har da cewa ba a tura sunan Sanata Rufa’i Sani Hanga zuwa hukumar zaɓe a kan lokaci ba, don haka ya nemi kotu ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Post masu alaƙa

Kotun majistare ta fara sauraren shari’ar sojan gona mai mukamin CSP 

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wanda ake zargi da damfarar mutane da cewa shi babban jami’in Dan sandan ne.

Hisbah ta fara horas da sabbin jami’anta a Jigawa