Home » Kano: Saudiyya ta yi bikin cika shekaru 93 a matsayin dunƙulalliyar ƙasa

Kano: Saudiyya ta yi bikin cika shekaru 93 a matsayin dunƙulalliyar ƙasa

by Anas Dansalma
0 comment
Kano: Saudiyya ta yi bikin cika shekaru 93 a matsayin dunƙulalliyar ƙasa

Ofishin jakadancin Saudiyya a nan Kano ya gudanar da bikin cika shekaru 93 da kasancewar ta dunɗulalliyar kasa.

Bayan gabatar da wasu daga cikin ababan tarihi da nasarorin ƙasar ta saudiya ne, maigirma Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana godiyarsa ga ƙasar ta Saudiya bisa gudummuwar da ta bai wa Kano ta fannin kiwon lafiya, noma, ilimi da samarda ruwan sha a jihar.

Haka kuma gwamnan ya yabawa kasar ta Saudiya ta fannin karfafa gasar karatun alƙur’mani mai girma a tsakanin al’umma wanda Kano ta dade tana amfani da irin wannan tallafi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci kasar Saudiya da ta baiwa Kano gudummawa wajan gina jami’ar musulunci a Kano, tallafawa yara marayu wajan ilmantar dasu, da kuma fannin lafiya wanda ya ce shima yana buƙatar tallafin kasar ta Saudiya.

Ya kuma baiwa ofishin jakadancin tabbacin cigaba da basu dukkanin haɗin kan da ya da ce a yayin aikin hajji da ma sauran mu’amuloli a tsakanin al’umar jihar Kano da kasar ta Saudiya.

Bayan Jawabin mai girma Gwamnan ne, ofishin jakadancin ya gabatar da shaidar girmamawa ga wasu ma’aikata da abokan hurɗar ofishin, domin yabawa da aikinsu ciki harda Ahmadu Haruna zago shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano,

Manyan bakin da suka halarci bikin sun hada da gwamnan Kano, da mataimakin gwamnan Jigawa, da mataimakiyar gwamnan Kaduna da wakilan gwamnan Zamfara da na Gwambe, sai wazirin Kano wanda ya wakilci sarkin Kano, da Tajjuddin Aminu Ɗantata, da ɗankasuwa Ɗahiru Mangal,  da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Muhd Usain Gumel.

A ƙarshe an gudanar da rawa irin ta al’adar al’ummar ƙasar Saudiyya

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?