Home » An Kama Hanyar Gyara Lantarkin Najeriya

An Kama Hanyar Gyara Lantarkin Najeriya

by Halima Djimrao
0 comment

Ministan Lantarki ƙasar nan Bayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin haɓaka wutar lantarki ta kai migawat dubu 20 nan da shekarar 2026, kuma ta kai har migawat dubu 60 nan da shekarar 2060.

Ministan ya bayyana haka ne a ƙarshen makon nan a Osogbo babban birnin jihar Osun, lokacin da ya kai ziyara kamfanin dakon wutar lantarki na ƙasa.

Adelabu ya bayyana shirye-shiryen da ma’aikatarsa ta yi, na gajere da dogon zango don cimma burin haɓaka wutar lantarkin, da dakonta da kuma rarrabata a faɗin ƙasar nan.  

Ya ƙara da cewa nan da ƴan watanni masu zuwa za a samar da wasu ƙananan tashoshin wutar lantarki a ƙarƙashin shirin shugaban ƙasa na inganta wuta a tarayyar Najeriya.

Haka kuma Adelabu ya yi gargaɗin cewa duk ma’aikacin da aka kama yana yi wa gwamnati zagon ƙasa a ƙoƙarin da ta ke yi  a ɓangaren wutar lantarki, zai ɗanɗana kuɗarsa.

Ministan ya kuma bayyana cewa an kafa wani kwamitin binciken musababbin gobarar da aka yi kwanan baya a tashar dakon wutar lantarki ta jihar Kebbi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?