Home » Kano: Wasu matasa sun nuna bajinta a fannin ƙere-ƙere

Kano: Wasu matasa sun nuna bajinta a fannin ƙere-ƙere

by Anas Dansalma
0 comment
Kano: Wasu matasa sun nuna banjinta a wani shiri na ƙere-ƙere da CITAD ta shirya

Wasu matasa masu fiƙira sun samar da na’urar sarrafa rediyo da aka fi sani da transmitter da sinadarin iskar gas daga haidirojin, abin ban ruwa a gonaki da sauransu a ƙarƙashin wata horaswa da CITAD ta gudanar.

Wani matashi mai shekaru 17, Khalifa Aminu, ne ya ƙirƙiri na’urar sarrafa rediyo ta FM, da kuma wasu ‘yan biyu, ‘yan shekaru 12, Hassan and Hussaini Muhammad, da suka samar da iskar gas da za a iya amfani da ita wajen girki ta hanyar haɗa man fetur da ruwa da gishiri da alumun.

Sai kuma Mu’azzam Sani wanda ya ƙirƙiri motar da ake irin sarrafata da rimot.

Matasan sun ce sun kai yin nasarar ne bayan samun horaswa da kuma samar musu da kayayyakin da za su yi aikin.

A nata jawabin, shugaban kwamitin gudanarwa na CITAD kuma lakcara a jami’ar Maiduguri, farfesa Amina Kaidal, ta ce, ƙasar nan na da matasa masu fiƙira da za a ci moriya.

Shi ma, babban daraktan CITAD, Engr. Yunusa Zakari Ya’u, ya jaddada buƙatar a ƙarfafa wa matasa domin su zama masu ƙirƙira da amfanar da kansu da ma ƙasa bakiɗaya.

Inda ya ce; gwamnatin jihar Kano ta ba wa Khalifa tallafi domin yin karatu a ƙasar Kanada.

Ya kuma jaddada aniyar cibiyar wajen cigaba da yi wa matasa jagoranci domin ciyar da su gaba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi