Babbar kotun tarayya dake zaman ta a jihar Kano ta bada umarnin hana kama dan siyasar nan wato Musa Iliyasu Kwankwaso.
Tun bayan da kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan kano ta ce Nasiru Gawuna ne gwamnan Kano ba Abba Kabir Yusuf ba, Musa Iliyasu Kwankwaso yake yiwa gwamnatin bankada tare da yin wasu zarge-zarge ciki har da shirin gwamnatin na ranto kudade, domin ta tafi ta bar su da biyan bashi.
Musa Iliyasu Kwankwaso ne dai ya shigar da karar gwamnatin jihar kano da kwamishinan yan sanda na jihar kano, tare da rokon kutun da ta hana wadanda yake kara kama shi har sai kotun ta ji bahasin dalilin da yasa suke son kama shi.
A cikin Umarnin kotun mai kwanan watan 25 ga watan October, 2023, Kotun ta bukaci wadanda ake kara da kada su kama mai Kara (Musa Iliyasu Kwankwaso), sannan kowa ya tsaya a matsayinsa har sai kotun ta sauraren dukkanin bangarorin Shari’ar.