Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya amince Gwamnatin Tarayya ta biya Naira biliyan 18 ga Asusun Group Life Assurance domin raba wa ga iyalan sojojin da suka kwanta dama, wajen kare ƙasar nan.
Sojojin Najeriya da dama sun rasa rayukan su ne a yaƙe-yaƙen kare ƙasar nan daga Boko Haram, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar bayan neman ɓallewa daga Najeriya, wato IPOB da ke Kudu maso Gabas.
Tinubu ya bayar da wannan albishir ne yayin ƙaddamar da Gidauniyar Tallafa Wa Iyalan Sojojin da Suka Kwanta Dama, a wurin Ranar Tunawa da Mazan Jiya ta 24, a Fadar Shugaban, a Abuja.
Ya ce har yau akwai ɗimbin bashin da ke kan gwamnati na yi wa waɗannan mazan jiya godiya da sakayya, waɗanda suka sadaukar da kan su wajen tsaron ƙasar nan.