Wata yarinya ta rasa ranta sakamakon wani haɗari da ya ritsa da ita tare da tare da motar wani hakimin a kan titin Ɗan Gauro dake garin Fari a karamar hukumar Dawakin Kudu a ranar Asabar.
Wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na rana bayan da direbar motar hakimin ya bi hannu da ba nasa ba, wato one way.
Faruwan hadarin keda wuya, sai hakimin ya wuce da ita zuwa asibiti mafi kusa da su, inda daga bisani aka turasu asibitin Malam Aminu Kano, amma da zuwansu asibitin likitoci suka tabbatar da rasuwarta.
Sai dai iyayen wannan yarinya sun koka kan yadda hakimin bai sake waiwayar su ba har aka sallaci gawar, inda suka nemi abi musu haƙƙinsu.
Abokiyar aikinmu Zubaidah Abubakar Ahmad ta halaci zaman makokin ga abinda iyayen yarinyar ke fadi.
Wasu da abin ya faru a gabansu sun shaida mana abin da ya faru game da lamarin