Kwamishinan yaɗa labarai Baba Halilu Ɗantiye ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.
Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ƴan Kwamitin shirye-shiryen Ranar Zaman Lafiya ta Duniya da ƙaddamar da Mujallar zaman lafiya suka kai masa ziyara har ofishinsa.
Baba Ɗantiye ya yi bayani cewa hakki ne a wuyan kowace gwamnati ta samar da tsaro kuma ta kare rayuka da dukiyoyin talakawanta, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin jihar nan za ta yi duk mai yiwuwa don ta girka wani tsarin haɓaka zaman lafiya a faɗin jihar nan.
Haka kuma kwamishinan ya yi alƙawarin tallafa wa kwamitin ya shirya Ranar Zaman Lafiya ta Duniya cikin nasara kamar yadda za a yi a duka ƙasashen duniya.
Shi ma da yake tsokaci a madadin jagoran tawagar kwamitin, kuma shugaban gidan rediyon Kano Hisham Habib, Babangida Mahamuda Biyamusu ya ce an ɗora wa kwamitin nauyin shirya bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya a jihar wanda za a yi Alhamis 21 ga watan Satumba, da kuma ƙaddamar da Mujallar Zaman Lafiya.
Babangida Mahmuda Biyamusu, ya yi godiya da yadda kwamishinan ya tallafa wa kwamitin don ya cimma abubuwan da ya sa a gaba, duk dai a madadin Hisham Habib.
Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano wadda Darektan ayyuka na musamman Sani Abba Yola ya sanya wa hannu.