Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Atiku Abubakar, ya ɗaukaka ƙara zuwa kotun daga ke sai Allah-Ya-isa, yana mai neman a yi watsi da hukuncin da kotu ta yanke, wanda ya tabbatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka yi ranar 25 ga watan Fabarairu na shekarar nan ta 2023.
Atiku Abubakar ya kawo hujjoji 35 da yake so kotun ta yi la’akari da su don tabbatar da adalci, da kuma ƙalubalantar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC, saboda ta bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.
Haka kuma takardar ɗaukaka ƙarar ta nemi kotu da ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ta zartar domin kuwa a cewar sanarwar, kotun ba ta yi duba da hujjojin da aka gabatar mata yadda ya kamata ba.