KAROTA ta sami nasarar cafke wasu matasa 5 da ke sojan gona

Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta sami nasarar cafke wasu matasa biyar suna sojojan gona.

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau ta cikin wata sanarwa da Kakakin Hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Kofar Nai’sa ya sanya wa hannu kuma ya aikowa muhasa radiyo.

Kakakin na karota ya kuma bayyana cewa an jima ana kawo ƙorafi hukumar cewa jami’anta na matsawa al’umma da karɓe-karɓen kuɗiBayan zurfafa bincike a wannan rana an sami nasarar cafke mutum biyar daga cikin wadanda ake zargin

Nabulisi ya bayyana cewa Shugaban Hukumar ya ce za a dauki matakin gurfanar da su a gaban Yansanda domin zurfafa bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace

Insert

Shugaban ya raƙi al’umma da su ci gaba da bawa Hukumar KAROTA haɗin kan da ya dace domin gudanar da ayyukanta bisa tsarin doka da oda

Post masu alaƙa

Jigawa Za Ta Bai Wa Alhazai Abinci Sau Uku a Rana a Hajjin 2026

Namadi Ya Kaddamar da Shirin Fadada Ilimi yayin da SLU ta Yaye Dalibai Sama da 4,000

Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Jigawa Ta Taya Gwamna Namadi Da Musulmi Murnar Eid-el-Fitr