Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya kawo ziyara jihar Kano

A yau ne Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Kashim Shettima.

Kashim Shettima ya ziyarci Kano ne domin kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijon jihar Alhaji Abubakar Imam Galadanchi.

A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun sakataran yada labaran Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ta ce, Mataimakin Shugaban kasar zai samu tarba daga Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf.

Tun da sanyin Safiya dai ake ta dakon isowar Mataimakin Shugaban Ƙasar, amma har kawo lokacin haɗa wannan rahoto bai iso filin jirgin Malam Aminu Kano da ke nan Kano ba.

Post masu alaƙa

Kwalejin Fasaha ta Kogi ta dakatar da lakcarori 7 kan cin zarafin ɗalibai

AIG Garba Ahmed ya bukaci daliban Sakandaren ’Yan Sanda Dawakin Kudu su zama jakadu na gari.

Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da masu sha da dillancin miyagun ƙwayoyi a Kano – Anti-Phone Snatching Force.