Home » Kasashe 20 sun amince da wani tsari mai suna “Rome Process” domin daƙile ‘yan ci-rani

Kasashe 20 sun amince da wani tsari mai suna “Rome Process” domin daƙile ‘yan ci-rani

by Yasir Adamu
0 comment
Kasashe 20 sun amince da wani tsari mai suna “Rome Process” domin daƙile 'yan ci-rani

Sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 20 ne suka amince su kaddamar da wani tsari wanda ake kira “Rome Process” domin dakile ci-rani ba bisa ka’ida ba da safarar bil adama.

Taron kasa da kasa kan raya kasa da ci-rani a ranar Lahadi wanda tsari ne na kasar Italiya, ya karbi bakuncin manyan shugabanni da jami’an diflomasiyya daga kasashen Mediterranean, da kasashen Gabas ta Tsakiya da na yankin Gulf.

Firaiministan Italiya Giorgia Meloni ta karbi bakuncin mahalarta taron inda suka tattauna kan mafita mai dorewa wurin yaki da masu zuwa ci-rani ba kan ka’ida ba da kuma matakan da za a iya dauka wurin dakile shi. Kasashen da suka halarci taron da kuma kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da Asusun Bayar da Lamuni da Bankin Raya Kasashen Musulmi da Bankin Duniya sun amince da aiwatar da tsarin

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi