Wasu dauke da muggan makamai da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari zuwa gidan tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku da ke yankin Ola a karamar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa.
Uku daga cikin jami’an tsaron da suke aikin tsaro gidan sun gamu da munanan raunuka a sakamakon harin da ‘yan bindigan suka kai a ranar Asabar.
A cewar daya daga cikin masu tsaron, maharan sun yi ta kokarin kutsa kai zuwa cikin gidan amma sun gamu da tirjiya daga masu tsaron gidan.
A sanarwar da mai dafa masa kan harkokin hulda da jama’a, Mr Peter Ahemba a jiya Lahadi cikin wata sanarwa ya misalta harin a matsayin mummunar lamarin da ba za su lamunta ba.
Ya ce tunin gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su farauto maharan tare da tabbatar da gurfanar da su.