Kashi 40 Na Ƴan Najeriya Na Samun wutar Lantarki Na Awa 20 A kullum – Gwamnati

Gwamnatin tarayya ta bakin Ministan wutar lantarki Mista Adebayo Adelabu, ta bayyana cewa kaso 40 na ƴan Najeriya na samun wutar lantarki ta aƙalla awa 20 a kullum.

Ministan ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da aka yi duba akan nasarorin da ma’aikatar wutar lantarki ta samu cikin wannan shekara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ministan yace nasarorin da suka samu a sakamakon jajircewa ne. Ministan ya ƙara da cewa dole ne Najeriya ta yi ƙoƙarin samar da wuta a koda yaushe domin samun cigaban tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.

“Wannan ne yasa ƙasashe irinsu China, da ƙasashen nahiyar Turai suke kan gaba wajen haɓɓakar tattalin arziƙi” a cewar  Mista Adebayo.

 

 

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da yin barazanar garkuwa da Dagacin garin Bangare a Kano.

INEC ta sanya ranar nazari kan korafe-korafe Pantami, Aminu Abdussalam da saura ya takara

Tinubu zai karɓo sabon bashin fiye da dala biliyan 20