Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da barazanar yin garkuwa da Dagacin garin Bangare, da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar.
Rundunar ta ce waɗanda ake zargin, Aliyu Naziru Garba da Bashir Alhasan, dukansu masu shekara 20, an kama su ne bayan jami’an ’yan sanda sun gudanar da bincike tare da tattara bayanan sirri.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce dagacin, Malam Idris, ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Gezawa a ranar 26 ga Oktoba.
Ya ce Dagacin ya shaida wa ’yan sanda cewa a ranar 24 ga Oktoba, wani mutum da ba a san ko wanene ba ya kira shi ta waya, inda ya yi masa barazanar yin garkuwa da shi.
Sanarwar ta ce bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda sun fara bincike, wanda ya kai ga kama mutanen biyu.
Rundunar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi, kuma ana ci gaba da bincike kafin gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa jami’an bisa gaggawar da suka yi wajen gudanar da binciken, tare da jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci aikata laifuka ba.
Ya kuma buƙaci al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.