Kasuwar Katako ta Gombe ta sake yin mummunar gobara a karo na biyu cikin wata guda.
Sabuwar gobarar ta auku ne a daren Litinin, inda ta lalata shaguna da dama tare da dukiyoyi na miliyoyin naira. Rahotanni sun danganta lamarin da matsalar wutar lantarki a kasuwar, wadda kusa da tashar jirgin ƙasa da ke garin Gombe.
Wannan bala’i ya faru ne kwanaki 29 bayan da wani ɓangare na kasuwar musamman sashen tsofaffin ƙarafa da kayan gwangwan ya ƙone a ranar 17 ga Nuwamba, inda akalla shaguna 30 da dukiyoyi na sama da Naira miliyan 500 suka kone .
Haka nan kuma, a ranar 15 ga Disamba, 2025, wani ɓangare na kasuwar ya sake ƙonewa, lamarin da ya ƙara tsananta asarar da ’yan kasuwar, waɗanda ke dogaro da kasuwar a matsayin tushen rayuwarsu.
Da yake jajantawa kan lamarin, Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan gobarar, yana mai cewa abin na da raɗaɗi da tayar da hankali.
- An yi musayar wuta tsakanin ’yan sanda da ɓarayin mota a Abuja
- Tsohon Shugaban Alkalan Najeriya Ibrahim Tanko ya rasu
Gwamnan ya bayyana cewa girman asarar da aka tafka babban koma-baya ne ga ’yan kasuwa masu jajircewa da neman halal.
Ya jajanta wa dukkan masu shaguna da ’yan kasuwar da abin ya shafa, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin jihar na tare da su a wannan lokaci mai wahala.
Gwamna Inuwa Yahaya ya umarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA), tare da sauran hukumomin da abin ya shafa, da su gaggauta tantance ɓarnar da ta auku, da musabbabin gobarar, tare da samar da agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa.
Ya kuma yi kira ga mutanen da abin ya shafa da su kwantar da hankulansu, yana mai jaddada cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin rage musu asara tare da ƙarfafa hanyoyin kariya don hana sake faruwar irin wannan gobara a nan gaba.
Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah Ya kare Jihar Gombe baki ɗaya, Ya kuma ba wa duk waɗanda abin ya shafa haƙuri da juriya
