Hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta gano gonaki uku da ake shuka ganyen wiwi a jihar Katsina.
Mataimakin shugaban hukumar mai kula da harkokin gudanarwa a jihar, Halilu Hamidu ne ya tabbatar da wannan nasara bayan samun bayanai daga wasu mutane.
Hamidu ya ce wannan shi ne karon farko da hukumar ta gano irin wannan gonar a ƙauyen Sobashi na karamar hukumar Dutsi.
Ya bayyana cewa masu waɗancan gonaki suna amfani da su ne wajen shuka tabar ta wiwi ta hanyar fakewa da noman kayan lambu irinsu tattasai da tumatur.
Jami’in ya ƙara da cewa hukumar ta kama mutum ɗaya sannan tana bibiyar sawun sauran abokan huldarsa.
A cewar hukumar wannan shi ne karon farko da ta gano gonakin shuka wiwi masu yawa a jihar ta Katsina.
Sannan hukumar ta kama sinadarin Kodin da darajarsu ta kai Naira miliyan goma.
NDLEA ta kara da cewa ba karamin hadari wadannan miyagun kwayoyin suke da su ba ga al’umma
Katsina na daya daga cikin jihohin Najeriya da ke iyaka da Jamhuriyar Nijar, inda masu fasaƙwaurin haramtattun kayayyaki ke safararsu a tsakanin kasashen biyu wanda hakan a ya sa hukumin ƙasar Nijar kokawa a kwanakin baya.