Kocin Ƙungiyar Kwallon Ƙafar Napoli Ya Ƙi Amincewa Ya Sayar da Osimhen

Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Napoli, Aurelio De Laurentiis, ya ce ba zai sayar da Victor Osimhen ba a cikin kasuwar bazarar nan ta musayar ‘yan wasa, a daidai lokacin da manyan kungiyoyi irin su Bayern Munich da PSG da Manchester United da Chelsea da Arsenal ke rububin sayo shi.

Osimhen ya taimaka wa Napoli ta Italiya lashe kofin gasar Serie a karon farko cikin shekaru 33 bayan ya jefa kwallon canjaras a raga a karawarsu da Udinese a ranar Alhamis.

Yanzu haka shugaban na Napoli ya ce, yana da shirin ci gaba da rike zaratan ‘yan wasansa har zuwa kaka mai zuwa kuma zai tsawaita kwantiragin kocin kungiyar Luciano Spalletti kamar yadda ya fadi.

Post masu alaƙa

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Mai Shekaru 30 Da Katunan ATM 88

Abubuwa shida da suka sauya tun bayan zaɓen Najeriya na 2023

Kanawa mazauna Abuja sun gudanar da babban taro