Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta dakatar da hukomomin EFCC, ICPC da DSS, daga tsare tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, har sai kotun ta yi nazari kan takardar koken da hukumomin suka shigar a gabanta.
Alkalin kotun mai Shari’a Donatus Okorowo, ya bayar da umarnin a kan takardar korafin da aka gabatar wa da kotun.
“A bisa wannan koken, kotu ta dakatar da hukomomin EFCC, ICPC da DSS, daga tsare zababben sanata Yari, har sai kotun ta sake zama bayan ta yi nazari kan kararrakin da ake tuhumar Tsohon gwamna, Abdul’aziz Yari”
Okorowo ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga wannan watan.