Wata babbar kotun tarayya mai zamanta a garin Gwarimpa da ke babban birnin tarayya Abuja ta tura tsohon ministan ƙwadago Chris Ngige a gidan yarin Kuje.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da tsohon ministan a gaban mai shari’a Mariam Hassan bisa tuhume-tuhume guda takwas da suka danganci cin hanci da rashawa.
Ngige, wanda ya kasance minista a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya isa harabar kotun ne da misalin ƙarfe 8:10 na safiyar yau Juma’a tare da rakiyar jami’an EFCC.
Hukumar ta zargi Ngige da aikata laifukan ne a lokacin da yake minista, musamman a lokacin da yake kula da hukumar bayar da tallafi ta Najeriya wato NSITF.
A tuhuma ta farko, ana zargin cewa daga Satumban 2015 zuwa Mayun 2023, Ngige ya yi amfani da matsayinsa a lokacin matsayin tsohon minista wajen bai wa abokansa cin gajiyar kwangila ba bisa ka’ida.
Sai dai a zaman kotun, tsohon ministan ya musanta laifukan da ake tuhumarsa da su.
Mai shari’a Mariam ta ɗage shari’ar zuwa Litinin domin sauraron buƙatar neman belinsa, sannan ta bayar da umarni a tsare shi a gidan yarin Kuje har zuwa ranar.
