Kotun ma’aikata ta kasa da ke Abuja ta umarci Bankin (GT) da ya biya korarren shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimingado, Naira miliyan 5,713,891.22 daga asusun albashi na gwamnatin jihar.
Adadin kudaden da Rimingado ke bin gwamnatin ne na albashin ma’aikata, bayan dakatar da shi a watan Yulin 2021.
Majiyarmu ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta dakatar da Muyi Magaji Rimingado ne bayan bude bincike kan wasu kwangiloli da ake zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan.
A zaman da aka ci gaba da yi a ranar Talatar da ta gabata, Bankin ta bakin lauyansa Joshua Shekwolo ya shaida wa kotun a cikin wata takardar neman sahalewa cewa gwamnatin jihar Kano tana da asusun ajiyar banki da jimillar kudaden da suka kai Naira miliyan5,713,891.22
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a O.O Oyewumi ya umarci GTBank ya biya kudin a asusun Rimingadon cikin sa’o’i 48.
An bayar da umarnin ne bayan gazawar gwamnatin jihar wajen mutunta hukuncin da kotun ta yanke a ranar 14 ga Disamba, 2022, inda ta bayar da umarnin biyan da kuma amincewa da Rimingado a matsayin halastacen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jahar Kano