Home » Nassarawa: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 17 Kan Zargin Garkuwa da Mutane

Nassarawa: ‘Yan Sanda Sun Kama Mutane 17 Kan Zargin Garkuwa da Mutane

by Anas Dansalma
0 comment

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta yi nasarar kama mutane goma sha bakwai da ake zargi da ayyukan garkuwa da mutane don karbar kudin fansa.

An samu nasarar kama wadanda ake zargin da garkuwa da mutane ne a ayyukan sintiri da samame da ‘yan sanda suka yi tun daga watan Fabrairu zuwa watan Afrilun wannan shekara ta 2023.


Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nasarawa, DSP Ramhan Nansel wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce a yayin gudanar da aikin nasu, sun kuma yi nasarar kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su, tare da kwace bindigogi hudu da albarusai takwas daga wasu wadanda ake zargin.


Ya kara da cewa binciken da suka gudanar ya nuna cewa wadanda aka kama, suna tare babbar hanyar Nasarawa Eggon zuwa Akwanga da ma cikin garin Lafia da kewaye zuwa Kudancin jihar, inda kuma suke sace mutane.


A makon da ya gabata ne tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Farfesa Onje Gye Wado ya kubuta daga hannun wadansu da suka yi garkuwa dashi.


A wata tattaunawa da shi, tsohon Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa wadanda suka yi garkuwa da shi matasa ne da ke sana’ar kiwon dabbobi.
A cewarsa, ba ya zaton talauci ne ko rashin aikin yi ne ya sanya su shiga sha’anin garkuwa da mutane.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?