Home » Kotu Ta Yarje Wa Jam’iyyun LP da PDP Duba Kayayyakin Zaɓe

Kotu Ta Yarje Wa Jam’iyyun LP da PDP Duba Kayayyakin Zaɓe

SIYASA/ATIKU

by muhasa
0 comment

Babbar katun daukaka kara ta kasar nan, ta bai wa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam’iyyar labour party peter obi izinin su binciki kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da babban zaben shekarar 2023.

‘Yan takarar biyu sun bukaci kotun da ta tilasta wa hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ta INEC, basu damar duba kayan zaben da aka yi amfani da su, ciki har da sakamakon da na’urar BVAS ta dauko, don su dauki hujjojin da zasu gabatar wa kotu a karar da suke na kalubalantar zaben da aka gudanar na shugaban kasa.

Mai taimaka wa jam’iyyar PDP a fannin yada labarai, Yusuf Dingayadi, ya ce hurumin da kotu ta basu abin farin ciki ne da zai taimaka musu wajen samo kwararan hujjoji da zasu gabatar wa kotu don neman a soke nasarar da Bola Tinubu na APC ya samu.

Ya kara da cewa suna sa ran za a gano kurakuran da aka yi a lokacin zabe, da kuma yadda aka kauce wa tsarin hukumar zabe.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kotu ta bawa jam’iyyun siyasar kasarnan damar shigar da karafinsu na bibiyar sakamakon yadda aka gudanar da zaben.

Matakin bibiyar sakamakon zaben na faraway ne daga katun daukaka kara har zuwa kotun koli.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi