Kotun kolin Nijeriya ta yanke hukunci kan dokar samun yancin bayanai ta shekarar 2011 ( FOIA) inda ta tabbatar da cewa dokar tana aiki ne a dukkan matakan gwamnatin tarayya, jahohi da kuma kananan hukumomi.
Hukuncin kotun kolin ya kawo karshen kin biyayya ga dokar yancin samun bayanai daga wasu hukumomin jahohi da cibiyoyi ke yi, inda suke fakewa da rashin fahimtar dokar da suka yi, cewa tana aiki ne kawai a hukumomin gwamnatin tarayyya.
Kungiyar yaki da rashin adalci da bibiya kan shugabanci nagari, ta bayyana gamsuwarta kan hukuncin da kotun kolin ta yanke a matsayin babban ci gaba ga damukuradiya.
Shugaban kungiyar Kwamared Umar Ibrahim Umar, ya yabawa juriyar da kotun kolin ta yi kan danbarwar da ta biyo bayan neman samun yancin bayanai ga yan kasa.
- Gwaji Ya Tabbatar Ma’aikatan Asibitin AKTH Sama Da 20 Basa Dauke Da Zazzabin Lassa
- An Sace Motar Malam Nuhu Ribadu
Kotun kolin ta gyara kuskuren da kotun daukaka kara ta yi, a shekarar 2018 na cewa dokar FOIA tana aiki ne kawai a matakin gwamnatin tarayya, kuma an yi hukuncin ne a shari’ar da Austin Osaku da kuma Edosaca , ya shigar a kara mai lamba SC/614/2014, inda kotun ta ce yayi daidai da kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin jahohi da kananan hukumomi su daina kin bada bayanai yayin da aka nema, tare da cewa yanzu babu wani dalili na yin jinkiri.
Haka zalika kungiyar ta kara da cewa, wannan hukuncin zai karfafawa kungiyon fararen hula, yan jarida da al’umma gwiawa wajen bibiya kan yadda ake kashe kudaden gwamnati karkashin dokar yancin samun bayanai a matakan gwamnati.