Babban ɗakin taron ƙasa da ƙasa dake Abuja da aka canzawa suna zuwa Bola Ahmed Tinubu International Conference Center ya laƙume Naira Naira biliyan 39.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu tare da ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, suka kaddamar da ɗakin taron da tsohon shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida ya gina a 1991.
Zunzurutun kuɗaɗen da aka ce an kashe na cigaba da ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, lura da irin halin Ni ‘yasu da waɗansu ɓangarori ke ciki a ƙasar.
- Iran Ta Harba Makamai Masu Linzami 100 Isra’ila, Mutane 40 Sun Jikkata
- Wasu Batagarin Matasa Sun Lalata Kayan Aikin Ginin Ofishin Civil Defense A Kano.
An kashe Naira biliyan 39, adadin ya ninninka Naira miliyan 240 da gwamnatin shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ta kashe yayin gina dakin taron a shekarar 1991, har sau 162.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta wallafa ta ce, kuɗaɗen da aka ce an kashe a gyaran ginin ya kai ace an gina Asibitoci 312 da Ajuujjuwa 1,200.