IDF, Avichay Adraee mai magana da yawun rudunar sojin Isra’ila ya ce Iran ta harbo wa ƙasar su aƙalla makamai masu linzami 100.
Adraee ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce an kakkaɓo akasarin makaman da ƙasar Iran ta harbo musu.
- Wasu Batagarin Matasa Sun Lalata Kayan Aikin Ginin Ofishin Civil Defense A Kano.
- Tinubu Ya Yi Farin Ciki Da Ricikin Jam’iyun Adawa
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin makaman da aka harbo basu samu isa wuraren da aka so ace sun kai ba.
Hukumomi a fannin kiwon lafiya na Isra’ila sun ce mutane 40 ne harin ya shafa wanda a yanzu suke karɓar kulawa a asibitoci daban daban, kuma biyu daga ciki na cikin mawuyacin hali. Kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa ta wallafa.