Mazauna Unguwar Karkasara Babban Giji karamar hukumar Tarauni a Jihar Kano, sun zargi wasu masu dillacin miyagun kwayoyin da yunkurin haifar musu da fitina da kuma kawo cikas ga ci gaban yankin.
Gamayyar mutanen unguwar sun koka ne bayan da wasu batagarin matasa suka lalata kayan aikin ginin ofishin Civil Defence da shugabancin karamar hukumar zai samar a yankin.
Tun a ranar Alhamis ne wasu matasa suka farfasa Bulon da sauran kayan aikin da aka kawo filin wanda ya zama matattarar saida miyagun kwayoyi wanda barazana ce ga tarbiyar yayansu.
A cewarsu abaya ana tara bola a wajen kuma tana cutar da su, inda suka nemi hukumomi don dakatar da zubarwa kuma aka hana baki daya, inda suka bukaci a yi musu wani abu da zai kawo ci gaba musamman ga matasa.
A baya dai karamar hukumar ta yi kokarin yi musu wajen koyar da sana’a don matasa su samu abinda za su dogara da kansu.


Sai dai sun kara da cewa wasu batagarin matasa ne suka dinga yin abubuwa marasa kyau, inda a yanzu karamar hukumar Tarauni ta amince a gina musu ofishin Civil Defence ,sai dai wasu sun farfasa kayan aikin ginin .
Sun dai bukaci shugabancin karamar hukumar da ya yi abunda ya dace na daukar mataki tsattsaura kan wadanda suke son haifar da fitina a unguwar tunda babu wanda yafi karfin hukuma.
Wani ladanin masallaci a yankin ya ce duk lokacin da ya fito yin kiran sallah yana cin karo da matasa dabam-daban kuma suna siyar da miyagun kwayoyi kuma yana yi musu nasiha amma sunki dainawa.
Haka zalika sun ce idan aka gina musu ofishin zai kara tsaron uunguwar , amma wadanda suke aikata munanan abubuwa basa son ci gabansu , domin sune suke kawo dillalan miyagun kwayoyin ana siyarwa da matasa maza da mata.
Filin dai yana jikin makarantar yan mata dake uunguwar Karkasarar , kuma a lokuta da dama wasu na haura cikin makarantar inda kayan koyo da koyarwa na makarantar yake cikin hadari.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto bamu sa mu ji daga bakin shugaban karamar hukumar Tarauni , Ahmed Ibrahim Muhammed, ba sakamakon bamu same shi ba, kuma wayarsa tana kashe, amma mataimakinsa ya ce zai nemi izinin yin Magana da shugaban karamar hukumar.