Gwamnatin jihar Filato da ke arewacin Najeriya ta ce mutane 14 sun mutu, yayin da ake zargin wasu 441 sun kamu da cutar kwalara tun bayan barkewar cutar a watan Yunin wannan shekara.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Nicholas Ba’amlong, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a birnin Jos, kan halin da ake ciki da kuma matakan da gwamnati ke ɗauka domin shawo kan cutar.
Ya ce cikin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar, mutane 20 an gano sun kamu da cutar ta hanyar gwajin gaggawa (RDT), yayin da mutane shida aka tabbatar da a dakin gwaje-gwaje.
Kwamishinan ya ce cutar ta bazu zuwa unguwanni 25 da ƙauyuka 107 a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa a yanzu haka marasa lafiya uku ne ke karɓar magani a asibiti, kuma duk a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
A cewar Dr Ba’amlong, an fara gano barkewar cutar ne a ƙaramar hukumar Mangu, wadda ta zama cibiyar da cutar ta fi ƙamari.
Ya ce Mangu ta samu mutane 53 da ake zargin sun kamu, ciki har da 10 da gwajin RDT ya nuna suna da cutar, sannan hudu aka tabbatar da su a dakin gwaje-gwaje, yayin da mutane 10 suka mutu.
Sai dai ya ce a yanzu babu wani sabon mai fama da cutar a Mangu, inda aka samu rahoton mutum na ƙarshe a ranar 22 ga watan Yulin 2026.