Ana Fargabar Ɓullar Zazzaɓin Lassa A Gombe

An samu rahoton wasu mutane huɗu da ake zargin sun kamu da cutar zazzaɓin Lassa a Jihar Gombe, sa’o’i kaɗan kafin ƙaddamar da shirin ‘Ranar Ba Da Gudunmawar Jini’  wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar.

Majiyoyi daga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Gombe sun bayyana cewa, daga cikin mutanen huɗun da ake zargin har da matar wani tsohon Kwamishina da kuma wasu mutum uku.

A halin yanzu, ana tsare da marasa lafiyar domin kulawa ta musamman yayin da hukumomin lafiya ke ƙara ƙaimi wajen tabbatar da sahihancin zargin ta hanyar gwaje-gwaje a ɗakin bincike.

Wata majiya da ba ta bayyana sunanta ba ta kuma nuna damuwa kan ƙarancin magunguna, inda ta ce allurai guda biyu ne kawai ake da su a halin yanzu, kuma wasu daga cikin magungunan ma sun riga sun ƙare wa’adinsu.

Sai dai har yanzu hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance domin tabbatar ko musanta waɗannan zarge-zarge ba.

Dangane da wannan lamari, ana shirin buɗe cibiyar killace marasa lafiya a Kwadon domin kula da waɗanda ake zargi da cutar tare da hana yaɗuwarta zuwa sauran al’umma.

Post masu alaƙa

INEC ta bayyana dalilin cire wasu ’yan takarar gwamna daga jerin sunayen da ta fitar

Ƙungiyar agoya bayan  shugaba Tinubu a zargi yan Daba da hana ta kai tallafi ga marasa galihu a Bauchi .

Gwamnatin Binuwai ta rufe makarantu 2 kan tilasta wa iyaye sayen litattafai